News
Dakarun Soji Sun Kama Mutum Da Manyan Makamai Da Kayayyakin Ƙera Bama-bamai A Hanyar Kaduna
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama wasu manyan makamai da kayayyakin da ake zargin na ƙera bama-bamai ne, a wani samame da suka kai a kan hanyar Kaduna zuwa Jos, a jihar Kaduna.
A cikin wata sanarwa, sojojin sun bayyana cewa an gudanar da samamen ne da misalin ƙarfe 11:45 na safiyar ranar Alhamis, a yankin Manchok, kusa da makarantar Boys Science Secondary School, yayin wani aikin tsayawa da binciken ababen hawa.
Mutane 4 Sun Mutu, 53 Sun Jikkata A Sakamakon Hatsarin Mota A Kano
Rundunar ta ce dakarun Operation Enduring Peace, tare da haɗin gwiwar wata tawagar musamman, sun tare wata mota kirar Opel Wagon mai launin shuɗi, wadda ke ɗauke da fasinjoji bakwai.
Bayan binciken da aka gudanar, jami’an tsaron sun gano harsasai guda 569 na bindigar yaƙi da jiragen sama, da wasu manyan abubuwan fashewa masu saurin tafiya, da kuma kwandunan harsasai guda 189 na alburusai nau’in 7.62mm da aka ɓoye a cikin motar.
Sanarwar ta kuma ce an gano wasu tsofaffin wayoyin salula a cikin kayan, waɗanda masana ke dangantawa da amfani da su wajen haɗa na’urorin fashewa na zamani (IED), musamman waɗanda ake sarrafa su daga nesa.
Direban motar, mai suna Khalifa Bawa, ya shaida wa jami’ai cewa kayan da ake zargin an ba shi su ne domin kai su wani wuri, sai dai bai iya bayyana wanda ya aiko da su ko wanda za a kai wa ba.
Rundunar ta ce an tsare dukkan mutanen da ke cikin motar tare da kayayyakin da aka kama domin ci gaba da bincike, yayin da hukumomin tsaro suka fara ƙoƙarin gano asalin su da inda aka nufa da su.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
