Connect with us

News

DIYYAR NAIRA BILIYAN ƊAYA: Ko Kwandala Ba Zan Ba Yahaya Bello —Natasha Akpoti-Uduaghan

Published

on

Natasha Akpoti 750x430

Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta ce ba za ta biya diyyar Naira biliyan 1 ga tsohon gwamnan jihar ba, Yahaya Bello.

Kotun wadda ke zamanta a Lokoja ce ta ba da umarnin bayan shigar da ƙara da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya yi gabanta kan zargin Natasha da ɓata masa suna.

Advertisement

Kaso 85 Na Mata Da Ƙananan Yara Na Mutuwa Sanadin Zazzaɓin Cizon Sauro ‎ ‎ ‎ — Rahoto

Ƙarar na zuwa ne bayan zargin sanatar da yin wasu kalamai a lokacin shirin talabijin Arise News mai suna “The Morning Show”.

Advertisement

Kotun ta yanke hukunci kan cewa waɗannan kalamai ɓata suna ne ga Yahaya Bello.

A yayin da take mayar da martani, Mrs Akpoti-Uduaghan, ta yi magana a ƙarƙashin wani rubutu a Facebook da hukumar EFCC ta yi kan shari’ar da take yi da Bello na zarginsa safarar kuɗi da ya kai Naira Biliyan 80.2.

Advertisement

A kalaman da ta yi, sanatar ta yi watsi da hukuncin kotun da kuma cewa ƙarara ba za ta biya Bello ko sisi ba a matsayin diyya.

Ta rubuta: “Ya ku hukumar EFCC, ku yi sauri. Shin kun san a jiya ya nemi diyyar Naira biliyan 1 daga babbar kotu a jihar Kogi? Ku ji wai yana tunanin zan biya shi kuɗin ne domin ya ƙara kan kuɗaɗen da ya sace waɗanda zai dawo da su? Shasha, ko kwandala ba zai gani ba.”

Advertisement

Wannan rubutu nata da ta rubuta da cike da shaguɓe ya karaɗe ko’ina nan da nan wanda ya jawo ce-ce-ku-ce.

A yayin da wasu da dama ke yaba mata kan matakin da ta ɗauka, suna masu cewa abu ne da ya shafi siyasa, wasu kuma na sukar ta kan yadda kalamanta suka zama raini ga kotu.

Advertisement

 

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending