News
Babu Hujjar Alaƙanta Gwamnati Da Kisan Da Akayi a Kano — Kungiyar NDWG
Kungiyar Nigerian Democracy Working Group ta soki rahoton da Amnesty International ta fitar dangane da kisan mutane biyar da ya faru a Jihar Kano, tana mai cewa rahoton ya gaza yin adalci da kuma gudanar da cikakken bincike kafin danganta lamarin da siyasa.
A wata sanarwa da Kodinetan kungiyar a Kano, Saed Adam Mohammed ya sanya wa hannu ranar 7 ga Mayu, 2026, kungiyar ta ce duk da tana Allah-wadai da asarar rayukan da aka yi, amma abin damuwa ne yadda Amnesty International ta yi gaggawar bayyana lamarin a matsayin rikicin siyasa ba tare da hujjoji sahihai ba.
Babu Hujjar Alaƙanta Gwamnati Da Kisan Da Akayi a Kano — Kungiyar NDWG
Kungiyar ta bayyana cewa bayanan da ake samu daga yankin sun nuna cewa rikicin da ya faru ranar 5 ga Mayu, 2026 arangama ce tsakanin wasu gungun matasa masu rikici da suka dade suna gaba da juna.
Ta ce har zuwa yanzu babu wata hujja da aka tabbatar a bainar jama’a da ke nuna hannu kai tsaye na gwamnatin Kano ko wasu jami’an siyasa a cikin lamarin.
Sanarwar ta kuma zargi Amnesty International da jingina rahotonta kan bidiyoyin da suka karade kafafen sada zumunta da kuma bayanan da ba a tantance ba, lamarin da kungiyar ta ce na iya haddasa rudani tare da bata sunan Kano a idon duniya.
“Abin takaici ne yadda rikicin da ake gani a matsayin rikicin masu aikata laifuka yanzu ake kokarin alakanta shi da siyasa, wanda hakan ka iya gurbata martabar jihar Kano da shugabanninta,” in ji sanarwar.
Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan abin da ta kira mayar da hankali fiye da kima kan Kano, alhali wasu sassan Najeriya na fama da matsalolin rashin tsaro, kashe-kashe da raba mutane da muhallansu ba tare da samun irin wannan kulawa daga Amnesty International ba.
Ta kara da cewa ci gaba da bayyana rikice-rikicen Kano a matsayin “ta’addancin siyasa” ba tare da cikakken bincike ba na iya bata sunan mutane da hukumomi marasa laifi.
Kungiyar ta yabawa gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa matakan da take dauka na dakile matsalar daba da tashin hankali tsakanin matasa, ciki har da shirin Safe Corridor na gyaran hali da horas da matasa masu tuba.
Daga karshe, kungiyar ta bukaci Amnesty International da ta rungumi adalci, gaskiya da kwarewa wajen fitar da rahotanni kan Najeriya, tana mai cewa rahotannin da ke dauke da son rai ba sa taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da karfafa dimokuradiyya.
Haka kuma ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin bisa doka.
