News
Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutum 5 A Kano
’Yan bindiga sun kai hari a yammacin ranar Litinin a ƙauyen ’Yankamaye da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano, inda suka kashe mutum biyar tare da jikkata wasu da dama.
Mazauna yankin sun ce maharan, wadanda yawansu ya haura 30, sun kutsa yankin ne da misalin karfe 6:00 na yamma a kan babura.
Shugaba Tinubu Na Tattaunawa Da Bankin Duniya Kan Sabon Bashin Dala Biliyan 1.25 —Rahoto
Aminiya ta ruwaito cewa sun shigo ne daga garin Rimaye da ke maƙwabtaka da su a Jihar Katsina, suna ta harbe-harbe babu ƙaƙƙautawa yayin da suke shiga garin.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun zo ne a kan kusan babura 12, inda kowanne babur ke ɗauke da mutum uku.
“Sun shigo daga Rimayen Katsina sannan suka fara harbe-harbe a cikin garin kafin sojoji su kawo ɗauki tare da fatattakar su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “Ya zuwa yanzu mun gano gawar mutum biyu sannan akwai wasu da suka samu raunuka. Mutane sun fara komawa gidajensu bayan sun tsere a jiya saboda harin.”
Ƙauyen ’Yankamaye, wanda ke kan iyaka tsakanin jihohin Kano da Katsina, ya sha fama da hare-haren ’yan bindiga, musamman a shekarar da ta gabata.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ba ta ce komai ba game da lamarin har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
