News
Jami’an NDLEA Sun Kama Ƙwayoyi Da Darajarsu Ta Kai Naira Biliyan 480
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya ta sake gagarumin kamu na ƙwayoyin da darajarsu ta kai naira biliyan 480 tare da kama ƴan asalin ƙasar Mexico.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NDLEA ya fitar a larabar nan, ta ce hukumar ta tarwatsa gungun masu safarar ƙwayoyi a Najeriya da Mexico.
Fubara Ya Janye Daga Neman Kujerar Gwamnan Rivers Karo Na Biyu
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyin ta ce ta gano haramtaccen kamfanin sarrafa ƙwayoyi, mafi girma da ta taɓa gani, a yankin Ijebu na jihar Ogun.
Baya ga gano kamfanin, NDLEA ta kama jagoran gungun masu safarar ƙwayoyin, da wasu ƙwararru a fannin ƴan asalin Mexico, sai kuma wasu shida da ke taimaka musu wajen gudanar da ayyuka.
A cewar shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, sun samu wannan gagarumar nasara ce bayan shafe tsawon watanni suna bibiya tare da samun bayanan sirri, inda suka ƙaddamar samame a jihohin Lagos da Ogun.
Wannan na zuwa ne ƙasa da makonni biyu, bayan nasarar da NDLEA ta samu haɗin gwiwa da hukumomin ƙasashen Amurka da Faransa da Girka da kuma Switzerland na tarwatsa wasu gungun masu safarar ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa.
