Connect with us

News

SCSN Ta Nuna Fushinta Kan Taɓarɓarewar Tsaro, Ta Buƙaci Gwamnati Ta Ɗauki Mataki Cikin Gaggawa

Published

on

IMG 20260507 WA0140

Majalisar Ƙoli ta Shari’a a Najeriya (SCSN) ta bayyana matuƙar damuwarta kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a sassa daban-daban na ƙasar nan, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa da za su kawo ƙarshen kashe-kashe, sace-sacen mutane da sauran ayyukan ta’addanci da suka addabi al’umma.

A cikin wata sanarwa da Sakatare Janar na majalisar, Malam Nafiu Baba Ahmad, mni, ya fitar a ranar 7 ga Yuni, 2026, SCSN ta ce ‘yan Najeriya na ci gaba da fuskantar rahotannin kashe-kashe, garkuwa da mutane, hare-haren ‘yan ta’adda da sauran munanan laifuka kusan a kowace rana, duk kuwa da tabbacin da jami’an gwamnati ke ci gaba da bayarwa.

Advertisement

NUJ Kano Ta Yi Alhinin Rasuwar Fitaccen Ɗan Jarida Adamu Ibrahim Getso ‎

Majalisar ta ce matsalar tsaro ta kai wani mataki mai tayar da hankali, inda ta yi nuni da hare-haren garkuwa da mutane da aka samu a jihohin Borno, Oyo, Neja da Zamfara, da kuma sace wani Janar mai ritaya tare da matarsa a Jihar Katsina.

Advertisement

A cewar majalisar, waɗannan al’amura kaɗan ne daga cikin bala’o’in da ‘yan Najeriya ke fuskanta a kullum, yayin da da dama daga cikinsu ba sa samun damar shiga kafafen yaɗa labarai.

SCSN ta ce rahotanni daga ƙungiyoyin sa ido kan harkokin tsaro da kare haƙƙin bil’adama sun nuna cewa dubban mutane sun rasa rayukansu, an yi garkuwa da su ko kuma sun rasa matsugunansu cikin ‘yan watannin da suka gabata. Har ila yau, rahotanni sun nuna cewa sama da mutum 1,000 aka yi garkuwa da su a Arewacin Najeriya cikin watanni ukun farkon shekarar nan kaɗai.

Advertisement

Majalisar ta nuna takaicinta kan yadda kiraye-kirayen da sarakuna, malamai, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki ke yi wa gwamnati domin ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a ba su haifar da sakamakon da ake buƙata ba.

“‘Yan Najeriya sun gaji da jawabai, alkawura, saƙonnin ta’aziyya da kwamitocin da ba sa haifar da wani sakamako a zahiri. Abin da ƙasar nan ke buƙata yanzu shi ne aiki mai ma’ana da sakamako a fili,” in ji sanarwar.

Advertisement

Majalisar ta jaddada cewa samar da tsaro ba wata kyauta ba ce daga gwamnati, illa babban nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata. Ta ce lokaci ya yi da waɗanda aka ɗora wa alhakin jagoranci za su tabbatar da sun sauke nauyin da ke kansu yadda ya kamata.

Sai dai SCSN ta yaba wa jami’an tsaro da dakarun rundunonin tsaron ƙasar nan bisa sadaukarwa, kishin ƙasa da jajircewarsu wajen kare Najeriya duk da ƙalubalen da suke fuskanta.

Advertisement

Haka kuma majalisar ta yi kira da a samar da cikakken bayani da gaskiya kan yadda ake kashe kuɗaɗen da ake warewa harkokin tsaro a kowace shekara. Ta ce an kashe tiriliyoyin naira wajen ayyukan tsaro, tattara bayanan sirri, sayen kayan aiki da gudanar da ayyukan soji, amma har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da ƙamari.

“‘Yan Najeriya na da haƙƙin sanin yadda ake amfani da waɗannan kuɗaɗe da kuma dalilin da ya sa har yanzu ba a samu ingantaccen sauyi ba duk da irin dimbin kuɗin da ake warewa,” in ji majalisar.

Advertisement

SCSN ta kuma buƙaci gwamnati ta rungumi sabbin dabaru masu ƙarfi wajen yaƙi da rashin tsaro, tana mai cewa tsofaffin hanyoyin da ake bi ba su samar da mafita ba. Ta ba da shawarar amfani da fasaha, ƙarfafa tattara bayanan sirri, haɗin gwiwar hukumomin tsaro, sa hannun al’umma da kuma inganta tsaron kan iyakoki domin murƙushe ayyukan miyagun laifuka.

Majalisar ta yi gargadin cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba da tafiya a wannan hanya mai haɗari ba, tana mai cewa jinin bayin Allah marasa laifi na neman adalci. Ta ce al’umma ba za su ci gaba da rayuwa cikin tsoro ba, manoma ba za su ci gaba da barin gonakinsu ba, haka kuma matafiya ba za su ci gaba da amfani da manyan hanyoyi cikin fargabar ko za su isa inda suka dosa lafiya ba.

Advertisement

“A yau ƙasa na buƙatar aiki, ba uzuri ba. Lokacin bayar da hujjoji ya wuce. Lokaci ya yi da za a nuna shugabanci nagari mai ƙwazo da jajircewa wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a Najeriya,” in ji sanarwar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending