News
Rashin Alfanun Kafa ’Ƴansandan Jihohi Ya Fi Fa’idodinsu Yawa — Farfesa Fagge
Masanin kimiyyar siyasa, Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya bayyana cewa ƙalubalen da ke tattare da kafa ’yan sandan jihohi sun fi fa’idodin da ake sa ran samu daga tsarin idan ba a shimfiɗa ingantattun matakan kariya da sa ido ba.
Farfesa Fagge ya bayyana hakan ne bayan wata tattaunawa da ya yi da gidan rediyon Premier Radio.
Dakarun Soji Sun Cafke Wanda Ake Zargi Da Ta’addanci, Sun Ƙwato Makamai A Kano
Ya ce duk da cewa masu goyon bayan tsarin suna ganin kafa ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen kusantar da harkokin tsaro ga al’umma tare da ba da damar magance matsalolin tsaro cikin sauri, akwai barazanar amfani da rundunar wajen cimma manufofin siyasa.
A cewarsa, babban abin da ke haifar da damuwa shi ne yiwuwar wasu gwamnoni su yi amfani da rundunar wajen murƙushe ’yan adawa, tsoratar da masu ra’ayin sabani ko kuma yin tasiri a harkokin siyasa a jihohinsu.
“Idan ba a samar da tsauraran dokoki da hanyoyin sa ido masu zaman kansu ba, akwai yiwuwar a karkatar da manufar rundunar daga aikin tabbatar da tsaro zuwa biyan wasu buƙatu na siyasa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa kafin aiwatar da tsarin, ya zama wajibi a samar da cikakken tsarin doka da kariya da zai tabbatar da cewa rundunar ba ta faɗa ƙarƙashin tasirin masu mulki ko wasu masu ruwa da tsaki.
Farfesa Fagge ya jaddada cewa duk wani sauyi da ya shafi tsarin tsaro a ƙasar nan ya kamata ya kasance bisa tanadin da zai kare dimokuraɗiyya, tabbatar da adalci da kuma kare haƙƙin ’yan ƙasa.
-
News6 days agoBan Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
