Connect with us

News

Gwamnatin Tarrayya Za Ta Sake Nazari Kan  Mafi Ƙarancin Albashi Na N70,000

Published

on

Advertisements
ads

Gwamnatin Tarayyar  ta bayyana cewa tana shirin sake nazarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata na Naira 70,000, tana mai cewa matakin ya zama wajibi saboda yadda yanayin tattalin arziki da tsadar rayuwa suka sauya.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan a wani taron da ƙungiyar Working People United (WoPU) ta shirya a Abuja.

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohon Shugaban APC  A Kebbi

A cewarsa, albashin Naira 70,000 da aka amince da shi a shekarar 2024 ba ya ƙara biyan buƙatun ma’aikata kamar yadda ake tsammani, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da matsin tattalin arziki.

Gbajabiamila ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta rage wa’adin sake nazarin mafi ƙarancin albashi daga shekara biyar zuwa shekara uku, domin tsarin ya riƙa dacewa da sauye-sauyen tattalin arziki.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta yi shawarwari da ƙungiyoyin ƙwadago kafin yanke hukunci kan sabon tsarin albashin.

Advertisement

A nasa ɓangaren, Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyadi, ya ce nasarar manufofin gwamnati na inganta walwalar ma’aikata za ta dogara ne kan yadda za a aiwatar da su cikin inganci.

Bayanan na zuwa ne a daidai lokacin da ma’aikata da ƙungiyoyin ƙwadago ke ci gaba da nuna damuwa kan yadda hauhawar farashin kayayyaki ke rage ƙarfin sayen albashinsu.

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending