Connect with us

News

Yadda jami’an Ƴansanda Sun  Kama Wani Fasinja Da Ya Ɓoye Bindiga A Cikin Burodi

Published

on

Advertisements
ads

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta kama wani fasinja da ake zargi da safarar makami, bayan jami’anta sun gano wata ƙaramar bindiga da aka ɓoye a cikin burodi yayin binciken ababen hawa da suka gudanar a birnin Fatakwal.

Kakakin rundunar, ASP Blessing Kaborlo Agabe, ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Juma’a, lokacin da jami’an ’yan sanda suka tsayar da wata motar haya domin gudanar da binciken tsaro na yau da kullum a kan titin Azikiwe, kusa da mahadar Red Riba da ke Fatakwal.

Ƙarancin Wutar Lantarki Ya Sa An Fara Bayar Da Hayar ‘Power Bank’ A Kano 

Ta ce yayin binciken motar, jami’an sun gano wata ƙaramar bindigar Browning da aka ɓoye cikin burodi, lamarin da ake zargin an yi da nufin kauce wa gano makamin a wuraren binciken jami’an tsaro.

A cewarta, binciken farko ya nuna cewa bindigar ba ta da lambar tantancewa, abin da ya ƙara jefa shakku kan asalinta da kuma manufar da aka yi niyyar amfani da ita.

Aminiya ta ruwaito cewa sun ce wanda ake zargin ya amsa cewa bindigar tasa ce, inda ya bayyana wa masu bincike cewa ya saya ta ne a garin Okrika kan kuɗi Naira 800,000.

Advertisement

Da yake tsokaci kan lamarin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ribas, Olugbenga Adepoju, ya ce gano bindigar da aka ɓoye cikin burodi ya nuna yadda masu aikata laifuka ke ci gaba da amfani da sabbin dabaru domin gujewa ganowa.

Ya yi kira ga al’umma da su kasance masu lura da duk wani mutum, kaya ko motsi da suke zargi, tare da gaggauta kai rahoto ga jami’an tsaro mafi kusa.

Kwamishinan ya kuma gargaɗi jama’a da kada su karɓa ko su ɗauki kayan da ba su san abin da ke cikinsu ba, yana mai cewa hakan na iya taimaka wa masu aikata laifuka ba tare da an sani ba.

Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai wajen daƙile safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending