News
Gwamnan jihar Rivers, ya sanya hannu kan kasafin kuɗi na shekarar 2024 da ya kimanin naira biliyan 800.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin jihar na shekarar 2024 da ya kimanin naira biliyan 800.
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan gabatar da kasafin a zauren majalisar dokokin jihar mai mambobi biyar, ƙarƙashin jagorancin Edison Ehie.
Sanatoci Sun Nemi A Rufe Hukumar AMCON Bayan Bacewar Naira Biliyan N146 Cikin Shekara Daya
Nan take ne kuma ‘yan majalisar suka gudanar da muhawara tare da amincewa da shi ba tare da ɓata lokaci ba, inda shi kuma gamnan ya sanya hannu a kansa yau Alhamis.
An gudanar da bikin sanya hannu kan kasafin ne a babban ɗakin taro na ofishin gwaman da ke harabar gidan gwamnantin jihar.
A ranar Talata ne dai wasu ‘yan majalisar dokokin jihar 27 suka bayyana ficewa daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar APC.
Bbc ta ruwaito cewa Lamarin da ya sa majalisar mai mabobi biyar ta ce ta kore su daga majalisar.
A ranar Laraba ne kuma gwamnan jihar ya bayar da umarnin ruguza ginin majalisar dokokin jihar, yana mai cewa an ɗauki matakin ne bisa dalilan rashin ingancin ginin.
To amma majalisar ta yi zamanta na ranar Laraba a gidan gwamnatin jihar, inda a nan ne aka gabatar mata da kasafin kuɗin jihar.
A wani labarin kuma Sanatoci Sun Nemi A Rufe Hukumar AMCON Bayan Bacewar Naira Biliyan N146 Cikin Shekara Daya
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
