Connect with us

News

Ɓarayi Sun Yi Awon Gaba Da Sarƙar Zinariya Mai Shekaru 2,500 Daga Gidan Tarihi

Published

on

gettyimages 2241780774

Ɓarayi sun sace wani tsohon abin wuya na zinariya mai kimanin shekaru 2,500 daga wani gidan kayan tarihi da ke garin Chatillon-sur-Seine a yankin Burgundy na ƙasar Faransa.

Masu gabatar da ƙara sun ce lamarin ya faru ne da rana tsaka, inda ’yan fashin suka fasa gilashin da aka ajiye kayan tarihin a ciki, sannan suka tsere da abin wuya.

Yan Bindiga Sun Sace Alkalin Babbar Kotu A Kebbi

Magajin garin, Jeremie Brigand, ya ce an taɓa yunƙurin satar kayan tarihin sau biyu a baya-bayan nan, lamarin da ya sa aka ƙara tsaurara matakan tsaro.

Sai dai ya ce a wannan karon ɓarayin sun zo da shiri wanda suka aiwatar cikin gaggawa duk da kasancewar ma’aikata, baƙi da jami’an tsaro a wurin.

Abin wuyan da aka sace yana da nauyin kusan rabin kilogram, kuma a zamanin Keltawa da Goliya ana amfani da shi a matsayin abin ado da ke nuna alamar iko.

Advertisement

Sarƙar wuyan na daga cikin tarin kayan tarihi na Vix Treasure, waɗanda aka gano a kabarin wata gimbiya a ƙauyen Vix a shekarar 1953.

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending