News
Hatsarin Mota Ya Janyo Cunkoso A Ƙarƙashin Gadar Shataletalen Dangi A Kano
An samu hatsarin mota a safiyar yau Talata a ƙarƙashin gadar Shataletalen Dangi da ke birnin Kano, bayan da wata mota ta kife yayin da take tafiya a kan hanyar.
Hatsarin ya janyo cunkoson ababen hawa na ɗan lokaci, lamarin da ya sa masu amfani da hanyar suka fuskanci tsaiko, sakamakon yadda motar ta toshe wani ɓangare na titin.
Kotun Daukaka Kara Ta Soke Hukuncin Da Ya Umarci INEC Ta Soke Rajistar Jam’iyyar ADC
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a san musabbabin hatsarin ba, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai kan yadda lamarin ya faru.
Haka kuma, ba a samu cikakken bayani kan ko akwai waɗanda suka rasa rayukansu ko kuma suka jikkata sakamakon hatsarin ba.
Ana kira ga masu ababen hawa da su riƙa bin dokokin hanya, su rage gudu, tare da yin taka-tsantsan domin kauce wa aukuwar irin waɗannan hatsarori.
