Connect with us

News

Kwamitin Tsara Kundin Yakin Neman Zaɓen Gwamnan Kano Ya Yi Taron Tsare-tsare Manufofin Ci Gaban Jihar A Kaduna

Published

on

IMG 20260831 WA0002

Kwamitin da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kafa domin tsara kundin yaƙin neman zaɓensa na wa’adin mulki na biyu, ya gudanar da taron kwana biyu a Jihar Kaduna.

Taron, wanda ya samu halartar mambobin kwamitin, ya mayar da hankali kan nazarin shawarwari da tsare-tsaren da mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano, ƙungiyoyin fararen hula (CSOs), ƙungiyoyin al’umma (CBOs), ƙungiyoyin ƙwararru da masana ilimi suka gabatar.

Tafiye-tafiyen Shugaba Tinubu Ya  Lakume Sama Da Naira Biliyan 37 —Bincike

A ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin, Dr Aminu Magashi Garba, mahalarta taron sun duba muhimmancin shawarwarin da aka gabatar, da yadda za a iya aiwatar da su, tare da tantance yadda za su dace da manyan manufofin gwamnatin Jihar Kano na inganta rayuwar al’umma.

Kwamitin ya kuma yi bitar nasarorin da aka samu a kundin wa’adin mulki na farko, tare da gano wuraren da ke buƙatar ƙarin kulawa da ingantawa domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a jihar.

A cikin wata sanarwa, kwamitin ya jaddada aniyarsa ta samar da kundin wa’adin mulki na biyu wanda zai mayar da hankali kan buƙatu da muradun al’ummar Jihar Kano, tare da gina sabbin tsare-tsare bisa nasarorin da aka samu a wa’adin mulki na farko.

Advertisement

Da yake jawabi, shugaban kwamitin, Dr Aminu Magashi Garba, ya ce kwamitin zai gudanar da tattaunawa da al’umma a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, domin sauraron buƙatu, damuwa da shawarwarin jama’a.

Ya ce yayin tattaunawar, kwamitin zai kuma gabatar da nasarorin da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samu a wa’adin mulki na farko, tare da bayyana muhimman alkawuran da aka tsara domin wa’adin mulki na biyu.

Dr Magashi ya bayyana cewa shawarwari da ra’ayoyin da za a tattara daga al’umma za su taimaka wajen tsara kundin wa’adin mulki na biyu ta yadda zai fi dacewa da buƙatu da muradun jama’ar Jihar Kano.

Ya kuma nuna godiyarsa ga mambobin Majalisar Zartarwa, ƙungiyoyin fararen hula, ƙungiyoyin al’umma, ƙungiyoyin ƙwararru, masana ilimi da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudummawar da suka bayar wajen aikin kwamitin.

Ya ce kwamitin zai yi amfani da abubuwan da aka tattauna a taron wajen ƙara inganta kundin, domin tabbatar da cewa ya ƙunshi manufofi da tsare-tsaren da za su amfanar da al’ummar Jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending