News
Dakarun Soji Sun Tarwatsa Ɗaliban Jami’ar AAUA Da Suke Gudanar Da Zanga-zanga
Jami’an Sojin Najeriya sun tarwatsa ɗaliban Jami’ar Adekunle Ajasin da ke Akungba-Akoko (AAUA) waɗanda ke gudanar da zanga-zanga, inda jami’an suka yi ta yin harbe-harben bindiga da amfani da hayaki mai sa hawaye.
Hakan ya faru ne bayan da ɗaliban suka rufe muhimman hanyoyi domin neman kawo ƙarshen yajin aikin da ya dakatar da harkokin karatu a jami’ar a ranar Alhamis
Za A Saki Wadanda Ba Su Da Laifi Da Hannu A Yunkurin Juyin Mulki —Ministan Tsaron Najeriya
Ɗaliban sun fito kan tituna ne domin nuna rashin amincewarsu da tsawaita yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da Kwamitin Haɗin Gwiwar Ƙungiyoyi (JAC)—wanda ya ƙunshi Ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU), Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’a (NASU), da Ƙungiyar Masana Fasaha ta Jami’o’i (NAAT)—suka duƙufa a duk faɗin makarantun gaba da Sakandare na Jihar Ondo.
Bidiyon da Daily Trust ta samu ya nuna sojoji sanye da kaki ɗauke da makamai suna korar ɗaliban tare da tarwatsa su a kewayen jami’ar.
Duk da kasancewar sojoji da kuma rahotannin yin harbe-harbe da amfani da hayaƙi mai sa hawaye, da yawa daga cikin ɗaliban sun ƙarfafa matsayarsu a farko, suna ɗaga kwalaye da aka rubuta “Yajin aikin ya isa”, yayin da suke neman a aiwatar da yarjejeniyoyin da aka ƙulla da ƙungiyoyin tare da biyan buƙatun albashin da ake bin ma’aikatan.
Da yake maida martani kan faruwar lamarin, Sakatare Janar na 18 na Ƙungiyar Ɗaliban AAUA, Tolulope Adeyefa, ya yi Allah-wadai da matakin da sojojin suka ɗauka, inda ya bayyana tura jami’an tsaro ɗauke da makamai kan ɗalibai masu zanga-zangar lumana a matsayin abin da ba za a aminta da shi ba.
A jerin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na ɗ, Adeyefa ya bayyana cewa ɗaliban suna amfani da haƙƙinsu ne na tsarin mulki wajen yin zanga-zangar lumana kan tsawaita rufe harkokin karatu da yajin aikin ya haifar.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
