Connect with us

News

Neman Kuɗin Aure Ne Yasa Na Shiga Harkar Garkuwa Da Mutane  —Wanda Ake Zargi

Published

on

1001118832

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta kama wasu mutane uku da ake zargi da kasancewa mambobin ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ta sace wata ’yar kasuwa a Ijedodo, tare da karɓar kuɗin fansa naira miliyan 21.

Waɗanda ake zargin su ne Semi Buawe, mai shekaru 35; Oluwatomi Obosi, mai shekaru 37; da Bamure Telemowei.

Jami’an Tsaro Sun Ceto Yara 15 Da  Aka Sayar A Kudancin Najeriya

An kama su ne bayan ’yan sanda sun bi sawunsu zuwa maboyarsu da ke Agadagba, a Jihar Ondo.

Binciken ’yan sandan ya nuna cewa ƙungiyar ta shirya garkuwar ne a Ondo, kafin ta koma Legas a watan Afrilun 2026 domin aiwatar da shirin.

An ce sun yi garkuwa da ’yar kasuwar ne a kusa da wani katafaren gida a Ijedodo, inda suka tsare ta a cikin daji na tsawon kwanaki uku kafin iyalanta su biya kuɗin fansa.

Advertisement

Buawe ya shaida wa masu bincike cewa ya taɓa shiga harkar garkuwa da mutane tun shekarar 2010, amma daga baya ya yi niyyar daina aikata laifin.

Sai dai ya ce shugaban ƙungiyar, wanda ake kira ID, ya nemi taimakonsa saboda ya san Legas sosai.

Ya ce daga cikin naira miliyan 21 da aka karɓa a matsayin kuɗin fansa, an ba shi naira miliyan 1.5.

Shi ma Obosi ya ce ya shiga harkar ne domin neman kuɗin da zai yi aure.

A cewarsa, bayan kammala aikin, an ba shi naira miliyan 2.5, wanda ya yi niyyar amfani da shi wajen fara sabuwar rayuwa.

Ya ƙara da cewa shugaban ƙungiyar ya karɓi naira 200,000 daga hannun kowannensu bayan sun koma Agadagba.

Advertisement

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, SP Abimbola Adebisi, ta tabbatar da kama waɗanda ake zargin.

Ta ce mutanen suna hannun ’yan sanda, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

 

 

LEADERSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending