Connect with us

News

Rikicin Boko Haram Ya Lalata Makarantu Fiye Da 5,000 A Borno —Gwamna Zulum

Published

on

unnamed 2021 10 28T154254.790

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ce sama da gine-ginen makarantu 5,000 ne suka lalace sakamakon rikicin Boko Haram da ya shafe sama da shekaru goma yana addabar jihar.

Zulum ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin ƙaddamar da wasu manyan ayyukan raya ƙasa a Maiduguri, babban birnin jihar, ciki har da makarantu, tituna da gadar sama.

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wani Mutum Ya Na Kokarin Sayar Da ‘Yarsa Yar Watanni 16

Ya ce a lokacin da rikicin ya yi kamari, kimanin yara miliyan 2.2 ne suka daina zuwa makaranta saboda rashin tsaro.

A cewar gwamnan, a wancan lokaci, adadin yaran da suka samu damar ci gaba da karatu bai wuce 500,000 ba.

Zulum ya kuma bayyana cewa rikicin ya yi sanadin mutuwar malamai da ma’aikatan makarantu da dama yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Advertisement

Ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da ƙoƙarin farfaɗo da harkar ilimi ta hanyar sake gina makarantu da samar da yanayi mai inganci da tsaro domin bai wa yara damar komawa makaranta.

 

 

THE CABLE 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending