Connect with us

News

Rundunar ‘Yansanda Ta Yi Gargaɗi Gam Da Yiwuwar Kai Hare-hare Makarantu Da Wuraren Ibada

Published

on

IMG 20260915 112054 036

Rundunar ’yansandan Nijeriya ta gargaɗi rundunoninta a faɗin ƙasar kan su kasance cikin shiri game da bayanan sirri da ke nuna yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a makarantu da wuraren ibada da sansanonin NYSC da sauran wuraren da ke cikin haɗari.

Wata sanarwa da Sashen Ayyuka na rundunar ya fitar, ta ce hare-haren na iya faruwa ne a daidai lokacin da aka fara zangon karatu na shekara ta 2026/2027.

Gwamnatin Sokoto Ta Bayar Da Umarnin Rufe Masallacin Sheikh Musa Lukuwa

Saboda haka, “rundunar ta umarci kwamishinonin ’yansanda da sauran sassan tsaro da su kara sa ido da sintiri da kuma binciken ababen hawa da mutane, tare da karfafa matakan tsaro a wuraren da ake ganin za su iya zama barazana na harin.”

Jami’an ‘yansanda sun ce ana zargin wasu ’yanbindiga da yin balaguro ta hanyar Katsina, Kaduna zuwa Jihar Filato, yayin da ake zargin wasu da ake dangantawa da mayaƙan ISWAP da abokan hulɗarsu na cikin gida kan cewa suna gudanar da bincike kan wuraren da suke shirin kai wa hari.

Hedkwatar Tsaro ta Nijeriya ta ce tana sa ido kan lamarin, yayin da hukumar NSCDC ta ce ta ƙara ƙarfafa tsarin tattara bayanan sirri da kuma tura jami’ai na musamman domin kare makarantu.

Advertisement

Masana tsaro sun buƙaci jama’a da su kasance masu sa ido tare da kai rahoton duk wani mutum ko abin hawa ko kuma wani yunƙuri da ba su amince da shi ba ga hukumomin tsaro.

Sun kuma buƙaci a ƙarfafa tattara bayanan sirri da ɗaukar matakan kariya tun kafin hare-hare su faru, musamman yayin da ƙasar ke tunkarar zaɓen 2027.

Ƙungiyar iyaye da malamai ta Nijeriya ta kuma yi kira da a ƙara matakan tsaro a makarantu, tare da amfani da fasahar zamani wajen gano abubuwan da ake zargi. Ta kuma buƙaci a farfaɗo da Shirin Kare Makarantu wato (Safe School Initiative) a ƙasar.

Duk da wannan gargaɗi dai, jami’an tsaro sun bukaci iyaye kan kada su bari tsoro ya hana su barin yara su koma makaranta, suna jaddada cewa kare makarantu na bukatar haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da makarantu da iyaye da kuma al’umma bakiɗaya.

 

TRT AFRIKA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending