Connect with us

News

Pantami Ya Lashe Sabon Zaɓen Dan Takarar Gwamnan Gombe A Jam’iyyar PDP

Published

on

5F46F8D0 7DA3 4F2B 8F36 33FCFD5F1696 770x400
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe sabon zaɓen dan takarar Gwamnan Jihar Gombe na Jam’iyyar PDP.

Pantami ya samu nasara a dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar, inda ya doke sauran ’yan takarar da suka fafata da shi a zaɓen.

Kotu Ta Yankewa Masu Garkuwa Da Mutane Hudu Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Khamisu Ahmed Mailantarki ne ya zo na biyu yayin da Usman Aliyu Garry ya zo na uku.

An gudanar da sabon zaɓen ne a yau Talata, 29 ga Satumba, 2026, bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe, wadda ta soke zaɓen fidda gwani na farko da ya samar da Pantami a matsayin ɗan takarar PDP na gwamnan jihar a zaɓen 2027.

Kotun ta umarci jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani cikin wa’adin da ta ƙayyade, bisa dokokin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokar zaɓe.

Advertisement

 

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending