Connect with us

News

Ƙofar Jirgin Sama Ta Ɓalle A Sararin Samaniya A Abuja

Published

on

IMG 20261016 173510 811

Wani jirgin sama mai zaman kansa samfurin CL60 ya yi saukar gaggawa a Abuja, bayan da ƙofarsa ta ɓalle jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin saman birnin.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026, lokacin da jirgin ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, zuwa Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammed da ke Legas.

Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci

Bayan faruwar lamarin, matuƙan jirgin sun aika saƙon gaggawa ga hukumomin filin jirgin saman Abuja domin neman izinin sauka cikin gaggawa.

Hukumar Binciken Haɗurra ta Nijeriya (NSIB) ta tabbatar da cewa ta fara bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.

Hukumar ta kuma bayyana cewa an gano ƙofar jirgin da ta ɓalle, yayin da ake ci gaba da bincike kan yadda lamarin ya faru.

Advertisement

 

 

TRT AFRIKA 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending