Connect with us

News

An Maka Shugaban Ƙaramar Hukuma A Kotu Kan Zargin Hana Ma’aikata Goyon Bayan Jam’iyyun Adawa

Published

on

kotu 768x390 (1)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

An maka Shugaban Ƙaramar Hukumar Ibi ta Jihar Taraba, Emmanuel Ubandoma, da majalisar ƙaramar hukumar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Jalingo, bisa zargin yi wa ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa barazana saboda goyon bayan jam’iyyun adawa.

Hajara Sule ce ta shigar da ƙarar a ranar 19 ga Oktoba, 2026, bayan yaɗuwar wani faifan bidiyo da ake zargin Ubandoma ya yi barazanar ɗaukar mataki kan ma’aikatan da ke shiga harkokin siyasa da ya bayyana a matsayin saɓawa muradun gwamnatin Gwamna Agbu Kefas.

Gwamnatin Kano Ta Rufe Cibiyoyin Lafiya Masu Zaman Kansu Guda 35 

A cikin ƙarar mai lamba FHC/JA/HR/66/2026, mai ƙarar ta roƙi kotun da ta tabbatar da haƙƙin ma’aikatan gwamnati na shiga jam’iyyun siyasa da suka zaɓa ba tare da tilastawa, tsoratarwa ko nuna musu wariya ba.

Ta kuma nemi kotun ta bayyana cewa barazanar hana ma’aikata albashi saboda goyon bayan wata jam’iyyar siyasa ta saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

An nemi diyyar Naira biliyan 20

Advertisement

Hajara ta shigar da ƙarar ne bisa sashe na 40, 42 da 46(1) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, da kuma wasu tanade-tanaden Yarjejeniya kan Hakkokin Ɗan Adam da Jama’a ta Afirka.

Ta buƙaci kotun ta hana Ubandoma, majalisar ƙaramar hukumar da wakilansu amfani da muƙamansu wajen tilasta wa ma’aikata shiga ko goyon bayan wata jam’iyyar siyasa.

Haka kuma, ta nemi a ba ta diyyar Naira biliyan 20 bisa zargin take haƙƙoƙin ma’aikata na ’yancin haɗuwa da ƙungiyoyi da gudanar da tarukan lumana.

Bugu da ƙari, ta buƙaci kotun ta umarci waɗanda ake ƙara da su bayar da cikakkiyar afuwa a bainar jama’a, ta hanyar wallafa ta aƙalla jaridun Nijeriya guda biyu.

Abin da aka ce shugaban ya faɗa

A cikin faifan bidiyon da ya yaɗu, Ubandoma ya gargaɗi ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa kan shiga harkokin siyasa da yake ganin sun saɓa wa muradun gwamnatin Gwamna Kefas.

Advertisement

An ruwaito shi yana cewa, “Idan kai ma’aikacin gwamnati ne ko kana riƙe da muƙamin gwamnati, na kama ka kana yin wannan abu, zan ɗauki mataki a kanka. Duk abin da ya biyo baya, ka rubuta shi a takarda.”

Ya kuma bayyana cewa bai kamata ma’aikaci ya riƙa yi wa gwamnatin da ke biyan sa albashi aiki, sannan ya shiga abin da yake ganin cin amanarta ne.

A cewarsa, bai dace ma’aikaci ya amfana da albashi da sauran abubuwan more rayuwa daga gwamnati, sannan ya aikata abin da yake ganin cin amana ne.

Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma ce ma’aikatan da ba za su iya raba alakar dangi da aikinsu na gwamnati ba su yi murabus.

Haka kuma, ya yi barazanar fallasa mutanen da ya zarga da cin amanar gwamnati kafin ƙarshen watan.

Abin da kundin tsarin mulki ya tanada

Advertisement

Sashe na 40 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanadi ’yancin ’yan ƙasa na haɗuwa da kafa ƙungiyoyi, ciki har da shiga jam’iyyun siyasa.

Sashe na 42 kuma ya tanadi kariya daga nuna wariya bisa dalilan da kundin tsarin mulkin ya ƙayyade, yayin da sashe na 46 ya tanadi damar neman kariyar kotu idan aka yi zargin tauye haƙƙoƙin asali.

Mai ƙarar ta nemi kotun ta tantance ko kalaman da ake zargin Ubandoma ya yi sun saɓa wa waɗannan tanade-tanaden kundin tsarin mulki.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana hukuncin kotu kan ƙarar ba.

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending