Connect with us

News

Ƙudirin Kafa ’Yan Sandan Jihohi Ya Samu Amincewar Jihohi 24

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Ƙudirin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na shekarar 2026, wanda zai ba da damar kafa ’yan sandan jihohi, ya samu amincewar majalisun dokokin jihohi 24 daga cikin jihohi 36 na ƙasar.

Wannan mataki ya cika sharadin samun amincewar aƙalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi, wanda ake buƙata kafin a iya kammala gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

Ƙudirin Kafa ’Yan Sandan Jihohi Ya Samu Amincewar Jihohi 24

Kwamitin Shugaban Ƙasa da ke kula da aikin kafa ’yan sandan jihohi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin, Femi Gbajabiamila, wanda kuma shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa.

A cikin sanarwar, kwamitin ya yaba wa majalisun dokokin jihohin da suka amince da ƙudirin, yana mai bayyana matakin a matsayin muhimmin ci gaba wajen sake fasalin tsarin tsaro a Nijeriya.

Haka kuma, kwamitin ya yaba wa Majalisar Dokokin Ƙasa bisa amincewa da ƙudirin a karatu na uku.

Advertisement

Sanarwar ta bayyana cewa za a mayar da kwafin ƙudirin ga Majalisar Dokokin Ƙasa domin kammala nazarinsa, kafin a miƙa shi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin tabbatarwa, bisa tanadin Sashe na 9 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

Idan aka kammala dukkan matakan da doka ta tanada, ƙudirin zai share fagen kafa tsarin ’yan sanda biyu a Nijeriya, wato na tarayya da na jihohi, ƙarƙashin shirin da aka bayyana da suna National Policing Bill, 2026.

Kwamitin ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da nazarin ƙudirin ta fuskar shari’a a Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya.

Ya ce ana sa ran za a mayar da ƙudirin ga kwamitin domin sake duba shi kafin ko a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026, kafin a miƙa shi ga Shugaban Ƙasa domin matakin ƙarshe.

A ƙarshe, kwamitin ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su bayar da cikakken haɗin kai domin tabbatar da nasarar aiwatar da tsarin kafa ’yan sandan jihohi a Nijeriya.

 

Advertisement

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending