Connect with us

News

Jami’an Ƴansandan Kano Sun Kama Wani Barawo Da Ya Sace Wayoyi 222 A Kasuwar Farm Centre

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Rundunar ’Yansandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 27 mai suna Abba Abubakar bisa zargin fasa shaguna huɗu tare da sace wayoyi 222 a kasuwar GSM ta Farm Centre da ke Kano.

Kakakin rundunar ’yansandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 11 ga Nuwamba, 2026.

Gwamnan Kano Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗi Na 2027 Na Sama Da Naira Tiriliyan 1.1 A Kano

Ya ce an kama wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 4:00 na safiyar ranar 7 ga Nuwamba a cikin rukunin shagunan City Centre Plaza, bayan jami’an tsaron kasuwar sun kai rahoton fasa shaguna ga ofishin ’yansandan Farm Centre.

A cewarsa, jami’an ’yansandan da suka isa wurin sun tarar da matashin yana yawo a cikin rukunin shagunan, dauke da abin yanka ƙarfe da sukandireba, inda suka kama shi bayan ya kasa bayar da gamsasshen bayani.

Sanarwar ta ce yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ya fasa shagunan huɗun tare da kwashe kayayyakin da ke cikinsu.

Advertisement

Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai wayoyin Android guda 127, wayoyin keypad guda 95, kwamfutar  Lenovo, kwamfutar hannu ta Samsung, na’urar sauti, inverter, power bank guda 29, na’urorin kunne guda 15 da sauran kayan haɗin waya guda 130.

Haka kuma, jami’an sun kwato kuɗi Naira 350,000 da wasu  wayoyin Android guda 17 da aka yi amfani da su.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending