Connect with us

Uncategorized

KANO: Jami’an Ƴansanda Sun Mutane Biyu Bisa Zargin Fashi Da Makami A Dajin Falgore

Published

on

WhatsApp Image 2026 11 10 at 18.13.16
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da addabar dajin Falgore da kewayensa da fashi da makami.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata, 10 ga Nuwamba, 2026.

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa

Ya ce an kama waɗanda ake zargin, Sulaiman Alhaji Umaru, mai shekara 35, da Abubakar Sale, mai shekara 22, a ranar 6 ga Nuwamba a yankin Dogon Dutse da ke dajin Falgore, bayan samun sahihan bayanan sirri.

A cewar sanarwar, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya amsa cewa ya haɗa baki da wasu mutum bakwai wajen yi wa wani Adamu Sa’adu fashi, inda suka ƙwace masa Naira miliyan 1 da dubu 350 da wasu kayayyaki.

Rundunar ta ce ta ƙwato Naira 600,000, wayoyin hannu guda tara, wuƙaƙe da sanduna daga hannun waɗanda ake zargin.

Advertisement

Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da tabbatar da cewa ana ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargin sun tsere.

Ya kuma ce za a gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu bayan kammala bincike, inda ya buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin yaƙi da laifuka.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending