Connect with us

News

Kenya za ta hukunta duk wanda ya ki sayar da masara a farashin gwamnati

Published

on

Yan kasar sun yi zanga-zanga kan tsadar kayan abinci

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

Gwamnatin Kenya ta ce za ta kama tare da hukunta duk wanda aka samu yana sayar da fakitin garin masara mai nauyin kilogiram 2 a sama da farashin sulai (shillings) 100 da aka kayyade.

 

Advertisement

A wani jawabi da ya yi ta talabijin a yau Alhamis Shugaba Uhuru Kenyatta ya jaddada umarnin da gwamnatinsa ta bayar na zaftare farashin da sama da rabin kudin da ake sayar da garin masarar a da sulai 205.

Zargin kalaman ɓatanci: A canja alƙalin da ke yin shari’a ta — Abduljabbar

Kakakin gwamnatin, Cyrus Oguna, ya gaya wa BBC cewa ana duba yadda za a biya ‘yan kasuwar da suka riga suka sayo masarar da tsada kafin a bayar da sanarwar rage farashin.

 

Wasu ‘yan kasuwar masu shaguna ba su fara sayar da masarar a sabon farashin da gwamnati ta tsayar ba saboda tsoron kada su yi asara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending