Connect with us

News

Sarkin Kano ya sabunta lasisinsa na tuƙi 

Published

on

Daga maryam Abdullahi muhmd

 

 

 

 

Mai martaba Sarkin Kano, Dakta Aminu Ado Bayero, ya sabunta lasisin tuki a hukumar kiyaye haɗurra ta kasa FRSC, a babbar cibiyar bada lasisin tuki da ke Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Kano.

Advertisement

 

Sarkin ya samu lasisin sa na farko a shekarar 1982, kamar yadda wata sanarwa da FRSC ga fitar a yau Talata .

Najeriya Ce Ta 18 A Gasar Tsere Da Tsalle-Tsalle Ta Duniya

Sanarwar ta fito ne daga bakin Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar Kano, CC Zubairu Mato, a Kano.

 

Sanarwar ta ce bayan ziyarar ban girma da Sarkin ya kawo; akwai bukatar sarakunan gargajiya su kwadaitar da talakawansu wajen aiwatar da lasisi.

Advertisement

 

“Aikin yi lasisin abu ne mai kyau kuma kyakkyawan misali, ne” in ji shi.

 

Hakanan ya nuna mahimmancin samun lasisin saboda yana iya zama katin shaida na mutum.

 

Tun da fari, Sarki Aminu ya ja hankalin jama’a da su rika tuka ababen hawa, babura masu ƙafa uku da aka fi sani da Keke Napep da babura da su yi lasisin su tare da sabunta su idan sun ƙare.

Advertisement

 

Ya kuma buƙaci sauran sarakinan gargajiya da su nuna alamar shugabanci su fito da kansu domin sabunta lasisi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending