Connect with us

News

Farashin kayayyaki sun ninka sau biyu a Zimbabwe

Published

on

Daga khadijah Abdullahi muhmd

 

 

 

 

 

Alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a Zimbabwe sun yi tashin gwauron-zabi zuwa ninki biyu da rabi, wanda shi ne adadi mafi girma da aka taba gani cikin shekara daya da rabi.

Advertisement

Daukacin ‘yan kasar na cikin matsanancin hali bayan karuwar farashin kayayyaki da suka rubanya har sau hudu, tun daga watan Fabarairu da ya gabata zuwa yanzu.

Rikicin PDP a Kano: Muhammad Abacha ya maka Sadiq Wali a kotu

Mahukunta a kasar sun dora alhakin matsalar kan nakasun tattalin arziki da cutar korona ta haifar, da tashin farashin makamashi da hatsi da kuma takin zamani a fadin duniya.

Karancin dalar Amurka a kasar domin shigo da kayan masarufi daga ketare ya sake ta’azzara tsadar kayyayaki da rayuwar ‘yan ƙasa.

A ranar Litinin da ta gabata ne babban bankin kasar ya fitar da sulallan gwal ga ‘yan kasuwa a wani yunkurin dakile hauhawar farashi da kuma karuwar bukatar dalar Amurka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending