Jirgin Emirates na Hadaddiyar Daular Laraba ya sanar da matakin rage zuwa Najeriya daga sau 11 a mako zuwa sau 7 a mako, daga 15 ga watan Agustan, 2022.
Emirates ya ce ya yanke wannan hukunci ne sakamakon maƙalewar kuɗaɗensa na cinikin tiketi.
Gwamnatin Najeriya dama na fuskantar matsin lamba kan datse kudaden kamfanonin jiragen ketare da yawansu ya kai dala miliyan 500.
