Connect with us

News

Mun ji sassauci bayan yanke masa hukuncin kisa – Mahaifan Hanifa

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

 

 

Mahaifiyar Hanifa Abubakar, yarinya mai shekara biyar da malaminsu ya kashe, na so gwamnati ta gaggauta zartar wa mutumin mai suna Abdulmalik hukuncin kisa da kotu ta yanke masa.

Advertisement

 

Cikin wata hira ta musamman da BBC Hausa, Murja Sulaiman Zubair ta ce “bayan yanke hukunci na ji sassaucin wani abin kuma alhamdulillahi”.

Jirgin Emirates zai rage jigilar fasinjoji a Najeriya

Shi ma mahaifin Hanifa, Abubakar Abdulsalam, ya ce ya samu natsuwa “tun da an yanke masa hukunci daidai da abin da ya aikata”, kuma ya gode wa mutane bisa addu’o’in da suka yi musu.

 

Babbar kotun da ke Jihar Kano a arewacin Najeriya ta yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa ne ta hanyar rataya bisa laifin kashe Hanifa da kuma ɗaurin shekara biyu kan laifin garkuwa da ita.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending