Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar wani ɗan ƙasar mazaunin Italiya inda aka zargi wani mutum da yi masa dukan tsiya a bainar jama’a ranar Juma’a.
Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NIDCOM) ta ce mutumin mai suna Alika Ogorchukwu mai shekara 39 ya gamu da ajalinsa ne lokacin da mutumin ya rufe shi da duka a yankin Civitanova Marche da ke Italiya.
Jirgin Emirates zai rage jigilar fasinjoji a Najeriya
“Lamarin ya faru a kan idon al’umma, inda ‘yan kallo suka taru har ma wasu suka ɗauki bidiyon abin da ya faru ba tare da sun damu da hana faruwarsa ba,” a cewar wata sanarwa da NIDCOM ta fitar a yau Asabar.
Sanarwar ta ƙara da cewa jakadan Najeriya a Italiya, Mfawa Omini Abam, ya yi Allah-wadai da kisan kuma ya miƙa ta’aziyyarsa ga Charity Oriachi, matar Alika.
Kazalika, jakadan ya ba da umarnin fara taimaka wa iyalan marigayin “don bi masa haƙƙinsa” sannan ya yi kira ga ‘yan Najeriya mazauna Italiya da kada su ɗauki doka a hannunsu.
