Mutum 16 da ake zargin ‘yan bindiga ne da ‘yan vigilante biyu sun mutu a bata-kashi tsakanin bangarorin biyu a garin Bangalala da ke karamar hukumar Wase a Jihar Filato.
Bangalala na da nisan kilomita 100 daga garin Wase, hedikwatar karamar hukumar.
Mukaddashin firaministan Iraƙi ya roƙi masu zanga-zanga su kwantar da hankulansu
Kauyukan da ke Wase na fama da hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane da shanu, abin da ya tilastawa mutane da dama tserewa daga gidajensu.
Rahotanni na cewa lamarin ya faru a kokarin jami’an sa-kai na vigilante kwato kauyen Bangalala da ke hannun ‘yan bindiga tsawon watanni.
Mazaunan yankunan dai sun tabbatar da wannan al’amari, sai dai jami’an tsaro ba su tsokaci ba kawo yanzu.
