Connect with us

News

An kama mutanen hudu da ake zargin sun taimaka wajen kai hari gidan yarin Kuje

Published

on

Indaranka logo

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

 

 

Jami’an tsaron Najeriya sun cafke wasu mutane hudu da ake zargin na kwarmata bayanan sirri ga ‘yan bindiga a babban birnin ƙasar, Abuja.

Jaridar PRNigeria ta rawaito wata majiya mai karfi ta hukumar leken asiri ta kasa da ke tabbatar da kamen.

Advertisement

Mutum 18 sun mutu a arangama tsakanin ‘yan bindiga da jami’an sa-kai a Filato’

Jaridar ta ce an cafke mutanen tare da wasu na’urori da makamai da tsoffin wayoyin hannu da basa amfani da intanet.

Majiyar da ke cikin ayarin mutanen da suka yi kamen na cewa, ana ci gaba da bincike cikin sirri domin gano shugabanninsu da masu daukar nauyinsu.

Waɗannan mahara ake kuma zargi da kai hari a wasu sassan yankunan Abuja, a cewar majiyar.

Yanzu haka ana tsare da mutanen da aka cafke da tuhumarsu domin amsa tambayoyi.

Jaridar ta kuma rawaito cewa hukumar tsaro ta Najeriya na tattara bayanan sirri domin gano masu hannu a matsalolin tsaro da hare-haren da ake kitsawa.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending