News
Haziƙar yarinya ƴar shekara 11 ta samu tallafin karatu daga Bankin Duniya
DAGA KHADIJA ABDULLAHI MAHMUD
Yarinya ƴar asalin jihar Kano mai shekaru 11, Saratu Garba Dan’Azumi, wacce take da baiwar lissafi, ta sami tallafin karatu daga Bankin Duniya, karkashin shirin AGILE.
Yarinyar wacce take aji 4 a firamare, ta dai na zuwa makaranta shekara ɗaya da ta wuce, ta ce ta sami damar iya lissafin ne bisa taimakon malamin lissafinta.
“ ƴan ajin mu suna kirana da ‘Turrum’ shi isa na daina zuwa makaranta, saboda bana son sunan,” in ji ta.
Ruwan sama ya hana ɗalibai zuwa makaranta tsawon kwanaki 3 a Jigawa
Yayin da jaridar Daily Trust ta kaiwa yarinyar ziyara a wani kauye da ke Ƙaramar Hukumar Gaya, an jarraba yarinyar da tambayar cewa idon da ta kai shekara 30 a duniya, kwana nawa tayi a duniya kenan, nan take ta amsa da cewa kwana 10,800, sanan aka kara mata da wasu tabbayoyin duka ta ansa su dai dai.
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
