Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Abubakar ya tabbatar wa masu yi wa ƙasa hidima a Sokoto cewa ba za a yi amfani da dokokin Shari’ar Musulunci ga waɗanda ba Musulmai ba.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sultan Sa’ad ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis a fadarsa, a lokacin da masu kula da harkokin ƴan bautar kasa karkashin jagorancin shugabansu suka kai masa ziyarar ban girma.
Tsawa ta faɗo tare da raunata mutum hudu a kusa da Fadar White House ta Amurka
Ya kuma tabbatar musu cewa za su samu tsaro duk da cewa akwai kalubale na tsaro a kasar baki daya.
Abubakar ya kara cewa za a kyale su su gudanar da addinansu.
Ya bayyana cewa ba za a dora wa wadanda ba Musulmi ba hukuncin Shari’ar Musulunci, kuma ya jaddada cewa babu wanda za a tursasa wa shiga Musulunci ba da son ransa ba.
“A Sakkwato, Shari’ar Musulunci ta sauka ne kawai a kan Musulmai, babu wanda zai tursasa masa saka hijabi, ko bin Shari’ar Musulunci idan ba Musulmi ba ne,” ya bayyana.
