News
Gwamnonin Najeriya Sun Shawarci Buhari Ya Kori Ma’aikatan Da Suka Haura Shekaru 50.
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Yayin da Najeriya ke fuskantar karancin kudaden gudanar da ayyuka da kuma biyan albashin ma’aikata, sakamakon matsalolin da suka addabi kasar, Gwamnonin kasar nan sun bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar korar duk wani ma’aikacin da ya zarce shekaru 50 a duniya.
Gwamnonin sun kuma bukaci Shugaba Buhari ya kara yawan harajin da talakawa ke biya, ciki har da sanya haraji a kan kowanne mutuum mai samun naira dubu 30 kowanne wata.
Jaridar Premium times ta bankado wannan shawara da gwamnonin suka gabatarwa shugaban kasa lokacin wani taro da suka gudanar da zummar lalubo hanyar samarwa gwamnati karin kudaden kashewa.
Shawarar gwamnonin ta kuma kunshi aiwatar da rahotan kwamitin Stephen Oronsaye wanda ya bukaci rufe wasu ma’aikatun gwamnati da basu da tasiri ko kuma wadanda ayyukan su ke cin karo da na wasu ma’aikatu.
Rahotanni sun ce gwamnatin tarayya Najeriya na da ma’aikata dubu 89 ne amma kuma tana kashe naira triliyan 4 da biliyan 100 wajen biyan su albashi da alawus alawus kowacce shekara daga cikin kasafin kudin naira triliyan 17 da ta ke yi a shekara.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
