News
Daga Karshe Buhari Ya Saki Dariye Da Nyame Daga Kurkuku
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Wata hudu bayan Gwamnatin Tarayya ta yi wa tsofaffin Gwamnonin jihohin Filato da Taraba, Joshua Dariye da Jolly Nyame, afuwa, daga karshe an sake su daga gidan gyaran hali.
An dai daure su ne tun da farko kan zargin karkatar da biliyoyin kudaden lokacin da suke jan ragamar jihohunsu.
Idan ba a manta ba dai kotun ta yanke wa Nyame daurin shekara 12 sakamakon samunsa da laifin karkatar da Naira biliyan 1.64 lokacin da ya ke Gwamnan jihar Taraba, yayin da Dariye aka yanke masa shekaru 10 sakamakon badakalar Naira Biliyan 1.26.
Wata majiya daga gidan yarin Kuje ta sanar da Aminiya cewa an sako tsoffin Gwamnonin ne da karfe 2:15 na ranar Litinin.
Haka zalika an sako wasu ukun daga gidan yarin Suleja da ke jihar Neja, bisa dalilan rashin lafiya, da tsufa, da kuma nuna kyawawan dabi`u a zamansu a kurkuku a cewar majiyar ta mu.
Duk kokarin da mu ka yi domin jin ta bakin Kakakin gidan yarin Abubakar Umar ya ci tura, sai dai wani jami`i ya tabbatar mana da cewa ya na gudanar da taro ne.
saoi kadan da bayyana wannan hukunci na Gwamnatin tarayya lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin al`umma, in da wasu suke ganin sam bai dace ba.
Daily Trust
