Connect with us

News

Ma’aurata Sun Yi Garkuwa Da Wata Mata Kan Zargin Maita

Published

on

Indaranka logo

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kotu ta tsare wani magidanci da ya daure wata mata a sarka na tsawon mako biyu saboda zargin ta da maita a Jihar Kwara.

 

Advertisement

Mutumin, mai shekara 40 ya aikata wannan aika-aikan ne tare da matarsa, inda suka karbi kudin fansa Naira dubu 100 daga hannun iyayen matar da suka daure.

 

Advertisement

 

Muzaharar Ashura: An Kashe Mana Mutum 6 A Zariya — ’Yan Shi’a

Advertisement

“Binciken farko ya nuna ma’auratan da sauran masu hannu a wannnan mummunan aiki ba su san darajar rayuwar dan Adam ba,” in ji dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Zacchaeus Folorunsho.

 

Advertisement

A yayin gurfanar da magidancin a gaban kotu, dan sandan ya shaida wa alkali cewa matar tasa ta tare da sauran masu hannu a laifin.

 

Advertisement

Ya bayyana cewa wadanda ake zargin, “Sun kware wajen aikata irin hakan a yankin Karamar Hukumar Wasu ta Jihar Kwara da kewaye.”

 

Advertisement

Saboda haka ya bukaci kotu da ta tsare mutumin, ya kuma samu amincewar Alkalin kotun, Majistare Ibrahim Dasuki.

 

Advertisement

Daga nan kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Agusta da muke ciki.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

AMINIYA

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending