Connect with us

News

Sha’aban Sharada ya fice daga APC, ya karbi tikitin takarar gwaman Kano a ADP

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Birni daga jihar Kano, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ta ADP, harma kuma ya samu tikitin takarar gwamnan Kano a zaɓen shekarar 2023 mai zuwa.

Daily Nigerian ta rawaito cewa, wata majiya ta tabbatar da cewa, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta tabbatar tsayawar Sha’aban takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADP, tare da wanda zai masa takarar mataimaki, Rabiu Bako.

Sha’aban dai yayi rashin nasara a hannun Nasiru Yusuf Gawuna a zaɓen fidda gwani na dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar APC, bayan zazzafan rikici da yayi da tsagin gwamna Ganduje karkashin shugabancin Abdullahi Abbas, har ya shiga tsagin G7 daga baya, kafin yanzu da ya fice daga jam’iyyar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending