News
Malam Ibrahim shekarau ya karyata labarinn ficewar sa daga NNPP zuwa PDP
Daga Yasir sani Abdullahi
Tsohon gwamnan kano Kuma senatan kano ta tsakiya Mai ci malan Ibrahim shekarau ya karyata ta labarinn da ,ake yadawa zai Fuce daga jam,iyyar NNPP zuwa PDP
Mai magana da yawun Sanata Shekarau Dr. Sule Ya’u Sule shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai cikin su har da kadaura24.
Dr. Sule Ya’u Sule al’umma su yi watsi da duk wani labari da ake yadawa game da Siyasar Gidan Sanata Malam Ibrahim Shekarau.
A cikin makon nan da muke ciki Zamu ba da cikakken bayani game da Siyasar Gidan Sanata Malam Ibrahim Shekarau saboda a wanke duk wani shakku a zukatan al’umma kan labaran da aka yada”. inji Dr. Sule Ya’u Sule
Da Sanyin safiyar talatar nan ne wata jaridar yanar gizo Mai suna Daily Nigerian ta rawaito shirin shekaran na ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar PDP sakamakon tayin da Atiku Abubakar ya yiwa shekaran.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
