News
Allah Ya Yi Wa Hakimin Rimi A Masarautar Katsina NUHU ABDULKADIR Rasuwa
Daga: Saifullahi Hassan Rimi
Basaraken ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a gidansa da ke karamar hukumar Rimi a jihar Katsina.
Wani cikin Iyalan Alhaji Aminu Nuhu Abdulkadir ya tabbatar da rasuwar basaraken a safiyar ranar Talata.
Za a yi jana’izarsa da rana kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Kafin rasuwarsa, Hakimin Rimi yana cikin Sarakuna 40 na Masarautar Katsina.
INDARANKA ta ruwaito cewa, basaraken ya yi bikin cika shekaru 40 a kan karagar mulkin Rimi kwanan nan.
Advertisements
