Connect with us

News

Gwamna Buni Ya Ba Iyalan Malamin Da Aka Kashe Aiki Yi

Published

on

Buni

 

Daga: Hamza Yusuf Abdulmumin

 

 

 

 

Advertisement

 

 

 

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayar da aikin yi kai tsaye ga ‘ya’yan marigayi malamin addinin Islama, Sheikh Goni Aisami da aka kashe a ranar Juma’ar da ta gabata a kusa da Gashua, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Gwamna Buni ya ba da umarnin ne a ranar Talata lokacin da ‘yan uwan marigayin suka ziyarce shi domin nuna jin dadinsu kan yadda ya ke nuna damuwarsa ga iyalan.

Gwamna Buni ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mamman Mohammed ya tabbatar da cewa gwamnati za ta tabbatar da gudanar da bincike kan lamarin mutuwar malamin.

Advertisement

Ya kuma ba da tabbacin gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa ‘yan uwan Mamacin domin sun yi asarar rashin Malamin

Malam Ibrahim Aisami, wanda ya yi magana a madadin ‘yan uwa, ya nuna jin dadinsa da sakon ta’aziyya da ziyarar da wata babbar tawagar gwamnati ta kai domin jajantawa iyalan.

Ya ce aikin zai rage wa iyalansu wahala sakamakon rasuwar malamin.

Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu mutane biyu da ake zargin sojoji ne suka kashe Sheikh Aisami.

A halin da ake ciki, ‘yan sanda sun kama wadanda ake zargin yayin da rundunar sojin ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike a kan lamarin domin bayyana cikakken bayani kuma duk wanda aka samu da hannu a kisan malamin zai fuskanci shari’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending