Connect with us

News

Asibitin koyarwa na Yobe zai fara aikin dashen ƙoda – Kwamishina

Published

on

Asibiti

Daga: Hamza Yusuf Abdulmumin

 

 

 

 

 

Advertisement

 

 

 

Dakta Mohammed Gana, Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Jama’a na Yobe ya ce nan ba da jimawa ba asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar, YSUTH, Damaturu, zai fara aikin dashen ƙoda.

Gana ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a Damaturu a yau Talat, cewa asibitin zai gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar Cibiyar Urology da Nephrology, na Jami’ar Mansoura ta ƙasar Masar.

Gana ya ce, haɗin gwiwar zai sanya likitocin cibiyar da za su ziyarci YSUTH domin gudanar da aikin dashen koda da kuma likitocin YSUTH da ke samun horo mai zurfi kan ilimin nephrology a cibiyar da ke Masar.

Advertisement

“Babban maganin ciwon koda shine dashen koda kuma mun san tsadar sa da wahalarsa.

“A saboda haka ne Gwamna Mai Mala Buni ya yanke shawarar samar da kayan aikin dashen koda ga YSUTH, tunda asibitin yana da karfin da zai iya amfani da su tare da horo mai kyau.

“Duk wadannan da nufin rage farashin maganin koda da kuma kawo taimako ga mutanenmu,” in ji kwamishinan.

Ya ce wankin ƙoda kyauta ne a asibitin, inda ya ce nan ba da daɗewa ba za a samar da sabbin na’urorin wankin ƙodar na zamani a garuruwan Gashua da Nguru, yankunan da cutar ta fi kamari.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending