Connect with us

News

Tunda ba’a cika min alkawari ba, na fasa janyewa Sha’aban takarar gwamna — Koguna

Published

on

Sha.aban

Daga: Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

 

 

 

Advertisement

 

 

 

Wani sabon rikici na shirin barkewa a jam’iyyar ADP reshen jihar Kano, wacce dan majalisa Sha’aban Ibrahim Sharada ya samu tikitin takarar gwamnan Kano, bayan ya tsallako cikinta daga jam’iyyar APC, sai dai kuma tuni dan takarar da ya janye masa, Nasiru Hassan Koguna, yace a dawo da Bako ya sha Kwai, domin kuwa an gaza cika masa alkawuran da aka dauka na sharuddan da ya gindaya kafin ya janye.

Cikin wata takarda da Koguna ya aikewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC, yace shi wanda Daliget 748 suka zaba a matsayin dan takara, amma kuma ya janyewa Sharada bisa wasu sharudda da suka hada da cewa, lallai za’a dawo masa da dukkan kudaden da ya kashe wajen neman takara da shirye-shiryen fara yakin neman zaɓe.

Ragowar sharuddan sun hada da bashi takarar mataimakin gwamna, kuma shi da kansa zai mika fom din INEC na janye takara ga uwar jam’iyya ta kasa, amma abin mamaki sai kawai gani yayi ana ta shirye-shiryen maye gurbinsa, dukda cewa yana raye ba mutuwa yayi ba, kuma sabuwar dokar zaɓe da aka yiwa gyara a 2022 ta bashi cikakkiyar dama, saboda haka yake sanar da cewa har yanzu shi ne halattaccen dan takara bisa doka da oda.

Advertisement

Sha’aban dai ya shiga ADP ne a baya bayan nan, bayan gumurzun rikici da suka tafka da tsagin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a jam’iyyar APC, wanda ya nemi tikitin takarar gwamna kuma ya sha kaye a hannun Nasiru Yusuf Gawuna, dukda Sha’aban din yace zaɓen nasu cike yake da lam’a kuma tabbas zai bi hakkinsa a gaban shari’a, kafin daga bisani kuma ya shiga jam’iyyar ADP.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending