Connect with us

News

Yaki ya ƙara zafi a Ethiopia yayin da Mayaƙan Tigray suka ƙwace iko da Kobo

Published

on

Ana ci gaba da yaƙi a arewacin Ethiopia

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Rahotanni daga Ethiopia na cewa ana ci gaba da yaƙi a yankin Amhara da ke arewacin ƙasar bayan rushe tsagaita wutar da aka yi na tsawon wata biyar a makon jiya.

 

Mayaƙan Tigray sun ƙwace iko da garin Kobo da ke yankin Amhara bayan da suka nausa Kudancin ƙasar kusa da kan iyaka.

Najeriya za ta karbo bashin tiriliyan 11 a shekarar 2023

Mazauna garuruwa da ƙauyuka da suka tattauna da BBC sun ce an ci gaba da faɗa a cikin tsaunukan da ke kusa dasu kuma kamar baza a daina ba.

Advertisement

 

A halin yanzu hukumomi a Woldia da Dessie- manyan garuruwan Amhara biyu da ke kusa da yankin sun ƙaƙaba taƙaitacciyar dokar hana fita da daddare.

 

Gwamnatocin Oromia da yankin Somali da ke gabashi sun bayyana goyon bayansu ga sojoji da yankunan Amhara da na Afar da ke fuskantar sabbin hare-hare.

 

A lokacin da ake ganiyar yaƙi a bara, yankuna da dama sun aika sojoji zuwa filin daga.

Advertisement

 

Akwai zarge-zarge da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta cewa faɗa na iya dawowa kan iyakokin Tigray da Eritrea mai maƙwabtaka.

 

Babban jami’in Tigray Getachew Reda ya yi ikirarin cewa jami’an rundunar sojin Habasha sun tsallaka kan iyakoki domin haɗa kai da Eritrea.

 

Zuwa yanzu dai BBC bata tabbatar da wannan ikirari ba.

Advertisement

 

Firamnista Abiy Ahmed wanda har yanzu bai fito fili ya yi magana ba tun bayan dawowar yaƙin, ya kai wata ziyarar aiki zuwa Algeria.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending