News
Al’ummomi a Neja da ke zaune kusa da madatsun ruwa na cikin mawuyacin hali
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Niger, ya ce al’ummomin da ke zaune kusa da madatsun ruwa da ke samar da hasken lantarki a jihar na cikin mawuyacin hali sakamakon rasa rayuka da kuma gidajensu ta dalilin ayyukan madatsun ruwan.
Gwamna Bello ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da hedkwatar hukumar madatsun ruwan da kuma motocin da za su yi aiki da su a Minna babban birnin jihar jiya Laraba.
Breaking news EFCC ta kama kakakin majalisar Ogun a filin jirgin saman Legas
Gwamnan ya ce samar wa da hukumar ofishin aiki zai basu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ya bukaci hukumar da ta kawo wa al’ummomin da suke ci gaba da fuskantar matsalar ambaliya sakamakon ayyukan madatsun ruwan agaji.
Advertisements
