Connect with us

News

Wani Rahoto Ya Bankado Yawan Bindigun Dake Hannun Mutane a Najeriya

Published

on

Bandiga

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

 

 

 

 

Advertisement

Wani rahoton Fasaha da cibiyar SBM Intelligence suka fitar ya nuna cewa akwai aƙalla bindigu miliyan 6 da dubu 154 dake yawo a hannun fararen hula a sassan Najeriya.

Jaridar Punch tace rahoton na SBM ya ƙunshi cewa Bindigun sun kai kashi 3.21 a duk mutum 100, yayin da adadin bindigu dubu 224 da 200 ke hannun rundunar sojoji da wasu 362,400 a hannun sauran hukumomin tsaron Najeriya.

Yan Sanda Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Ceto Dan Takarar PDP a Katsina.

An jingina yawaitar kananan makamai da yaɗuwar matsalar tsaron kasar nan, duk da faɗi tashin da gwamnati ke yi na ganin ta ɗaƙile lamarin a lokuta da dama.

Daga cikin irin hoɓɓasa da gwamnatin tarayya ta yi har da amince wa da kafa sabuwar cibiyar kula da ƙananan makamai, da zummar dakile yaɗuwarsu a cikin al’ummar ƙasa.

Haka nan kuma, majalisun tarayya sun amince da kudurin dokar kafa hukumar kula da kananan makamai da magance yaɗuwarsu tsakanin mutane ta ƙasa.

Advertisement

Amma har yanzun shugaban kasa bai rattaɓa hannu a kai ba.

A cewar wani shafin Intanet ‘Legal Advocacy Centre” idan shugaban kasa ya rattaɓa hannu a kudirin, zai bai wa hukumar damar zama kungiya mai zaman kanta, kuma hakan zai bata damar aiki yadda ya kamata.

Duk wani yunƙurin domin jin ta bakin kakakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, bai kai ga nasara ba domin ya ƙi amsa tambayoyin da aka aike masa kan batun har zuwa lokacin da muka haɗa wannan rahoton.

Wani masani kan harkokin tsaro, Timothy Avele, ya ce akwai bindigu a hannun mutane sama da yawan adadin da aka bayyana a cikin rahoton.

Ya kuma nuna shakku kan cewa ko da shugaban ƙasa ya rattaɓa hannun kan kudirin kafa hukumar, ba tabbas bane a samu wani banbanci.

Yace “”A ganina wannan bai haɗa da makaman da yankuna suka mallaka ba da wasu da ba’a san da su ba.

Advertisement

Babu ɗaya daga cikinsu da zai nuna banbanci na a zo a gani matukar mazauna na jin barazana da rashin tsaro.”

“Abun takaici ne yadda cin hanci ya mamaye iyakokin ƙasa da na ruwa wanda ya saukaka safarar irin waɗan nan kayayyaki masu haɗari zuwa cikin ƙasa.

Haka zalika, wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Dickson Osajie, yace adadin bindigun da aka gano hannun mutane wata alama ce dake nuna hadari ga kasar nan wacce ke shirin gudanar da babban zabe a 2023.

A ɓangarensa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana rahoton a matsayin wanda bai inganta ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending