News
An gano masana’antar da ake sayar da jarirai kan kudi N400,000 a Ogun
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar ‘Yan sanda ta jihar Ogun ta cafke wasu mata biyu da take zargi da bude wata masana’antar sayar da jarirai a Agbado dake karamar hukumar Ifo a jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar SP Abimbola Oyeyemi, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an kama matan biyu masu suna Christiana Iyama da Margaret Ogwu, a watan Agusta bayan da suka samu bayanan sirri daga al’umar yankin.
Kwadayin Kudi Ke Kai Wasu ’Yan Kwallon Firimiyar Ingila —Kroos
Binkicen farko ya nuna cewa Christiana Iyama tana daukar ‘yan mata ta rika hada su da maza domin su dauki ciki, da zarar sun haihu kuma sai ta sayar da jaririan ga masu bukatarsu a kan kudi kusan naira 400,000.
Christiana Iyama ta shaida wa yan sanda cewa ta sayar da jarirai uku ga wasu mata da ta samu ta wannan hanya
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umarci da a kai matan biyu sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar domin fadada bincike.
BBC NEWS
