News
Albania da Iran sun raba gari kan kutsen Intanet
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN
Albania ta bai wa jami’an diflomasiyyar Iran awa 24 su fice daga kasarImage caption: Albania ta bai wa jami’an diflomasiyyar Iran awa 24 su fice daga kasar
Albania ta yanke duk wata huldar diflomasiyya tsakaninta da Iran tare da umartar ma’aikatan ofishin jakadancin su fice daga kasar, kan zargin kutsen intanet.
Jariri da mutum hudu sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Yobe
An ambato firaiminista Edi Rama ya ce wani kwamiti ne ya gano kulla-kullar da kwararan shaidu da suka nuna Iran tayi hayar wasu kungiyoyi har hudu da za su kaddamar da kutsen ga gwamnatin Albania ranar 15 ga watan Yuli.
Masu kutsen sun yi kokarin kawo cikas a shafukan intanet da sace bayanai masu muhimmanci na gwamnati tare da gogesu.
Iran dai ta maidawa Iran martani da cewa zargin ba shi da tushe bare makama. A sanarwar da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi allawadai da zargin na Albania da matakin korar jami’an diflomasiyyarta, tare da cewa kamata ya yi su hau teburin tattaunawa don magance matsalar.
Amirka dai na allawadai da duk kasar da ta yi wa aminiyar kawancen NATO kutse ta intanet, tare da shan alwashin hukunta Iran kan abin da ta kira barazanar tsaro ga Albania.
Dangantaka tsakanin Tirana da Tehran ta dade da yin tsami, tun bayan Albania ta bai wa dubban ‘yan Iran mafakar siyasa, wadanda suka tsere daga gida saboda barazanbar da suke fuskanta
BBC NEWS
