News
Yan Sanda Sun Yi Ram Da Wani Likita Kan Mutuwar Direban
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Rundunar ‘yan sandan jihar Edo tayi hulin wani likita bisa mutuwar wani direban taksi a garin Benin babban birnin jihar.
Wanda ake zargin, Dokta Abass Adeyemi wanda ya fito daga karamar hukumar Offa ta jihar Kwara ana zarginsa da kashe direban taksin a ranar 3 ga watan Satumba, 2022, a cikin garin Benin tare da jefar da gawarsa a unguwar Otofure, bayan Oluku a karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabas.
Saudiyya na son daukar nauyin bikin baje-koli na 2030
Yayin da yake gabatar da wanda ake zargin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, ya ce Abass Adeyemi ya gana da mamacin, direban taksin dan asalin jihar Delta Emmanuel Agbovinuere a cikin garin Benin a cikin watan Yulin wannan shekarar a lokacin da yake gudanar da aikinsa.
A cewar Nwabuzor, daga baya sun zama abokan juna wanda shine dalilin da ya sa marigayin ya sake amsa gayyatar wanda ake zargin a ranar uku ga watan Satumba a lokacin da ya isa Benin domin yin sana’ar sa ta haya da motarsa.
Ya ce wannan shi ne karo na karshe da aka ga direban taksin da rai.
Wanda ake zargin wanda ya ki amsa tambayoyin ‘yan jarida, ya roki iyalan marigayin da suyi masa gafara.
Rundunar ‘yan sandan ta ce za a gudanar da cikakken bincike daga bisani za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.
Alkibila
.
