News
Shugabannin majalisa za su gana da Buhari kan yajin aikin ASUU
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugabannin Majalisar Wakilan Najeriya za su gana da Shugaba Muhammadu Buhari game da batun yajin aikin malaman jami’a ƙarƙashin ƙungiyar ASUU, wanda suka shafe wata kusan bakwai suna yi.
Wata sanarwa ta ce Kakakin Majalisa Femi Gbajabeamila ya ce nan da ‘yan kwanaki za su fitar da rahoton tattaunawar da suka yi da shugabancin ASUU da zimmar bai wa Buhari “don ya samu wasu bayanai na daban” don ɗaukar matakin da ya dace.
Za Mu Sanya Wa Jam’iyyu Ido Kan Kudaden Yakin Neman Zabe — INEC
Lamarin na zuwa ne yayin da ofishin ministan shari’a ya ce zai duba ƙorafin ASUU kan batun tsarin biyan albashi na IPPIS da kuma UTAS, wanda shi ne babban batun da ya jawo yajin aikin.
A ranar Alhamis ne shugabannin majalisar suka gana da ASUU, inda ministan ƙwadago da shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya da sakataren gwamnati suka halarta da zimmar kawo ƙarshen yajin aikin.
“Za mu rubuta matsayarmu da shawarwarinmu mu kai wa shugaban ƙasa, abin da ya sa muka taru ke nan don neman mafita,” a cewar Mista Gbajabeamila.
-
Opinion5 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion5 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News3 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
