Connect with us

News

Shugaban matasan PDP na kasa, Kadade ya shiga cikin fitattun mutane 100 a duniya

Published

on

Kadade

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

 

 

 

 

Advertisement

 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Wata kungiyar kwararru da ke kula da shugabanni masu tasiri a duniya, MIPAD, ƙarƙashin kulawar zauren majalisar dinkin duniya, ta zabi Hon. Muhammad Kadade Suleiman, Shugaban Matasa na PDP na Ƙasa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun mutane guda dari mafiya tasiri a shekarar 2022.

MIPAD ta aike wa da uwar jam’iyyar PDP, ta na mai sanar da ita zaɓen Kadade a matsayin ɗaya daga cikin fitattun mutane dari mafiya tasiri a shekarar 2022.

NDLEA ta kama ƙwayoyin Tramadol guda miliyan 13 a Legas

Shugaban matasan PDP na kasa Kadade na ɗaya daga cikin ƴan kwamatin zartaswar jam’iyyar PDP da aka zaɓa a shekarar da ta gabata a yayin babban taron jam’iyyar da ta zabi sabbin shugabanni.

Kasancewar shugaban matasan PDP na kasa, Kadade matashi ɗan shekaru 26, ya sanya zabensa ya ja hankali a ciki da wajen Najeriya.

Advertisement

Shi ne na farko mai karancin shekaru da ya taɓa rike irin wannan mukamin a tarihin jamiyyun siyasa a Najeriya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending